17 Agusta 2015 - 20:54

Da siyar yau litiin ne jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Ayatullah sayyid Aliyu Khamia'i ya gana da mahalarta taron kasa da kasa karo na 6 na cibiyar Ahlul baiti ta duniya inda ya bayana muhimmancin da cibiyar take dashi wajen yada koyarwar ahlul baiti da kuma bayyana ayyukansu a matsayin jahadi a tafarkin All.., har ila yau ya nuna cewa Amurka itace hakikanin abokiyar gaba a duniya iota da Haramtacciyar Kasar Isra'ila suna kunna wutar rikici tsakanin musulmi shia da sunna, dama tsakanin kasashe .

Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Ayatull.. Uzma sayyid Aliyul Khamina’I ya gana da mahalarta taron kasa da kasa na cibiyar ahlul baiti ta duniya nan birnin Tehran.

Da safiyar yau litinin ce ilahirin bakin da suke halartar taron kasa da kasa karo na 6 na cibiyar ahlul baiti ta duniya suka gana da jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar a husainiyar Imam Khumanin dake nan birnin Tehran, A lokacin ganawar jagoran ya bayyana cewa kalubalantar makircin kasashe ma’abota girman kai na duniya daidai yake da yin jihadi saboda All.. ya kara da cewa danganta cibiyar Ahlul bait da jagororin shirya na Iyalan gidan manzo All. Tsira da aminci su tabbata gareshi da iyalan gidansa yana da muhimmancin sosai, musamman wajen koyi da su da yada koyarwarsu da hukumce-hukumcen Addini da yaki da zalunci da babakere. Domin jihadi a tafarkin All.. ba wai da makami ba ne kawai ya shafi yakin na siyasa ala’adu tatalin Arziki ds.

Da yake bayani game da makircin da ma’abota girman kai na duniya jagoran yace  uwar shedanu Amurka itace babban misali na abokin gaba, domin ta yi nesa da wata kyakkyawar dabi’a ta dam Adamtaka kuma tanai yin amfani hanyoyin yaudara ta nuna shimfida fuska a gefe guda kuma tana tafka muggan laifuka. Ya ci gaba da cewa makiya suna amfani da hanyoyin cusa sabani tsakanin kabilu da alummomi, shi;a da sunna ,wanda ya fi muni a cikinsu shi ne tsakanin kasashe, sai dai baban abin takaici shi ne wasu daga cikin musulmi da basu da hangen nesa sun rudu da wannan parpagandar suna taimakawa makiya wajen cimma bakar aniyarsu,

Babban misali da ya shafi gwamnatoci kuwa shi ne kamar kasar Siriya halin yanzu, a lokacin da aka yi amfani da taken musulunci a kasashen Tunusiya da Masar wajen kifar da gwamnatocin dagotu sai kasashen Amurka da HKI suka fake da wannan wajen rusa kasashen dake gwagwarmaya da babakere da mamaye don haka nema suka sanya kahon zuka akan kasar siriya.288

Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Ayatull.. Uzma sayyid Aliyul Khamina’I ya gana da mahalarta taron kasa da kasa na cibiyar ahlul baiti ta duniya nan birnin Tehran.

Da safiyar yau litinin ce ilahirin bakin da suke halartar taron kasa da kasa karo na 6 na cibiyar ahlul baiti ta duniya suka gana da jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar  a husainiyar Imam Khumanin dake nan birnin Tehran, A lokacin ganawar jagoran ya bayyana cewa kalubalantar makircin kasashe ma’abota girman kai na duniya daidai yake da yin jihadi saboda All.. ya kara da cewa danganta cibiyar Ahlul bait da jagororin shirya na Iyalan gidan manzo All. Tsira da aminci su tabbata gareshi da iyalan gidansa yana da muhimmancin sosai, musamman wajen koyi da su da yada koyarwarsu da hukumce-hukumcen Addini da yaki da zalunci da babakere. Domin jihadi a tafarkin All.. ba wai da makami ba ne kawai ya shafi yakin  na siyasa ala’adu tatalin Arziki ds.

Da yake bayani game da makircin da ma’abota girman kai na duniya jagoran yace   uwar shedanu Amurka itace babban misali na abokin gaba, domin ta yi nesa   da wata kyakkyawar dabi’a ta dam Adamtaka kuma tanai yin amfani hanyoyin yaudara ta nuna shimfida fuska a gefe guda kuma tana tafka muggan laifuka. Ya ci gaba da cewa makiya suna amfani da hanyoyin cusa sabani tsakanin kabilu da alummomi, shi;a da sunna ,wanda ya fi muni a cikinsu shi ne tsakanin kasashe, sai dai  baban abin takaici shi ne wasu daga cikin musulmi da basu da hangen nesa sun rudu da wannan parpagandar suna taimakawa makiya wajen cimma bakar aniyarsu,

Babban misali da ya shafi gwamnatoci kuwa shi ne kamar kasar Siriya  halin yanzu, a lokacin da aka yi amfani da taken musulunci a kasashen Tunusiya da Masar wajen kifar da gwamnatocin dagotu  sai kasashen Amurka da HKI  suka fake  da wannan  wajen rusa kasashen dake gwagwarmaya da babakere da mamaye don haka nema suka sanya kahon zuka akan kasar siriya.